IQNA

Ba Za A Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Duniya A Aljeriya Ba Saboda Cutar Corona

17:30 - April 04, 2021
Lambar Labari: 3485782
Tehran (IQNA) za a maye gurbin gasar kur’ani ta duniya da gasar kur’ani ta cikin gida a Aljeriya domin kaucewa yaduwar cutar corona.

Gidan rediyon kasar Aljeriya ya bayar da rahoton cewa, Yusuf Bil Mahdi ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Ajeriya ya bayar da sanarwar cewa, za a maye gurbin gasar kur’ani ta duniya da gasar kur’ani ta cikin gida a Aljeriya domin kaucewa yaduwar cutar corona a tsakanin jama’a.

Ya ci gaba da cewa, za agudanar da gasar kur’ani ta cikin gida wadda za ta samu halartar fitattun makaranta da mahardata daga dukkanin sassa na fadin kasar.

Ya ce makaranta da mahardata 126 ne za su shiga wannan gasa wadanda za a zabo su daga cikin lardunan kasar, ta hanyar gudanar da gasar fitar da gwani

Sannan kuma ya kara da cewa, daga karshen gasar za a fitar da mutane uku ne wadanda suka fi nuna kwazo, wato na daya da na biyu da kuma na uku, domin ba su kyautuka na musamman tare da girmama sua  ranar 27 ga watan Ramadan, sannan kuma mutane 15 za su kai zuwa ga mataki na karshen gasar.

 

3962302

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fitattun makaranta tsakanin halartar
captcha