IQNA

Nujba Ta Iraki Ta Tabbatar Da Cewa A Shirye Take Ta taimaka Ma Hizbullah

20:08 - August 08, 2021
Lambar Labari: 3486181
Tehran (IQNA) Кungiyoyin gwagwarmayar a Iraƙi sun sanar da aniyarsu ta kasancewa tare da ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon.

A wata sanarwa da suka fitar ƙungiyoyin gwagwarmayar Iraƙi na Kata’ib Hizbullah da al-Nujaba waɗanda wani ɓangare ne na dakarun sa kai na ƙasar da aka fi sani da Hashd al-Sha’abi sun jaddada goyon bayansu ga ƙungiyar ta Hizbullah da kuma sanar da shirinsu na shiga yaƙi da ita idan har wani yaƙi ya ɓarke tsakanin ƙungiyar da haramtacciyar ƙasar Isra’ilan.

Har ila yau ƙungiyoyin biyu sun taya ƙungiyar ta Hizbullah murnar nasarar da ta samu na mayar da martani cikin lokaci da hare-haren da Isra’ila ta kai wasu yankuna na Kudancin Labanon.

Ita ma a nata ɓangaren ƙungiyar Ansarullah ta ƙasar Yemen ta jinjina wa ƙungiyar Hizbullah ɗin sakamakon mayar da martanin da ta yi wa haramtacciyar ƙasar Isra’ilan a jiya juma’a tana mai cewa hakan yana nuni da irin shirin da ƙungiyar Hizbullah ɗin take da shi ne na mayar da martani ga duk wani wuce gona irin Isra’ila a kan Labanon.

Har ila yau ƙungiyar ta sanar da shirin da ta ke da shi na kasance tare da dakarun ƙungiyar Hizbullah ɗin a duk lokacin da Isra’ilan ta yi gigin kawo wa Labanon hari.

 

 

captcha