Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, wasu mahara sun kai hari kan daruruwan mutane da suka taru a gaban ginin ma'aikatar shari'a da ke birnin Beirut na kasar Lebanon domin zanga-zangar nuna adawa da siyasantar da bincike kan fashewar da ta auku a gabar teku dake birnin Beirut a shekarar da ta gabata.
Maharan sun boye ne akan rufin wani gida dake makwabtaka da inda masu zanga-zangar suka taru a gaban ginin ma'aikatar shari'a dake yankin Tayouneh a birinin Beirut.
Kafin daga bisani suka fara kai musu hari wanda ya yi sanadiyar kashe mutane akalla 6 tare da jikkata wasu guda 37, sai dai jami'an tsaro sun samu nasarar damke daya daga cikin wadanda suka kai harin.
Rahotannin sun ci gaba da cewa wata mata na daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu bayan da aka harbe ta da harsashi a kai.
Ana zargin maharan su na da alaka da jam’iyar Labanese Forces party ta kasar, Kuma an ji karar fashewar wasu abubuwa guda biyu a daura da inda yamutsin ya auku.
Kungiyoyin Hizbullah da Amal ne suka bukaci magoya bayansu su gudanar da ganganmi domin nuna rashin amincewa da halin ko in kula da kan binciken da ma'aikatar shari'a take nuna kan bin kadun fasheawar da ta auku a birnin Beirut a bara.