IQNA

Lebanon: Saudiyya Ta Bukaci Abin Da Ba Zai Taba Yiwu Ba Kan Batun Hizbullah

20:16 - November 03, 2021
Lambar Labari: 3486508
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Lebanon ta ce Saudiyya ta bukaci abin da ba zai taba yiwuwa ba kan batun Hizbullah

Ministan harkokin wajen kasar Lebanon Abdullahi Bu Habib ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudiya ta shimfida wa kasar sharuddan da ba zamu taba cika su ba, wato kan yunkurin dakile kungiyar Hizbullah.

Tashar talabijin ta Al-Manar ta nakalto ministan harkokin wajen kasar ta Lebanon ya na fadar haka wa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa kasar Lebanon tana bukatar dangantaka da kasar Saudiya a matsayen ‘yantacciyar kasa ba wacce za’a umurceta ta yi a bunda take bukata ba.

Bu Habib ya kara da cewa Saudiya ta bukaci gwamnatin kasar Lebanon ta takaita matsayin kungiyar Hizbullah da tasirinta a kasar.

Daga karshe ministan ya kammala da cewa wannan bukatar ba zai taba faruwa ba, don kungiyar hizbullah kungiya ce wacce ake tafiyar da gwamnatin kasar Lebanon da ita, sannan tana da makamai wadanda bata amfani da su a kan mutanen kasar Lebanon.

 

4010132

 

 

captcha