IQNA

Harin Ta'addancin Kungiyar Al shabab Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8 A Somalia

20:53 - November 25, 2021
Lambar Labari: 3486605
Tehran (IQNA) harin ta'addanci da kungiyar Al shabab ta kai a birnin Mugadishu na kasar Somalia ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8.
Kungiyar ‘yan ta’adda ta Alshaba a kasar Somaliya ta dauki alhakin tada bom a wata makaranta a tsakiyar birnin Magadishu babban birnin kasar a safiyar yau Alhamis, wanda kuma yayi sanadiyyar mutane 8 daga ciki har da wasu ‘yan makaranta.
 
Kakakin ‘yansanda a birnin Abdifatah Adam Hassan ya sheda cewa banda mutane 8 da suka rasa rayukansu akwai wasu 17 wadanda suka ji rauni.
 
Kungiyar ta Alshabab ta bada sanarwan daukar alhakin harin ne ta tashar radiyonta wacce ake kira ‘Andulos’. Ta kuma kara da cewa tana nufin kai harin kan wasu jami’an gwamnatocin kasashen yamma ne wadanda suke ziyara a kasar, kuma wadanda sojojin tarayyar Afrika suke bawa kariya.
 
Wani mutum wanda yake inda abin ya faru ya fadawa AFP kan cewa jami’an tsaro masu zaman kansu ne suke bawa bakin kariya a lokacinda bom din ya tashi, sannan ya ga cewa mutane 4 daga cikin jami’an tsaron sun ji rauni a harin.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4016184
captcha