IQNA

Cikar Shekaru Biyar da Kisan Kiyashin Da Sojojin Myanmar Suka Yi Wa Musulmi Rohingya

15:35 - August 25, 2022
Lambar Labari: 3487744
Tehran (IQNA) dubban ‘yan gudun hijirar Rohingya ne sukayi wani gangami a wannan Alhamis tunawa da abunda suka danganta da kisan kiyashin da sojojin Myanmar sukayi masu a baya.
A Bangaladesh, dubban ‘yan gudun hijirar Rohingya ne sukayi wani gangami a wannan Alhamis tunawa da abunda suka danganta da kisan kiyashin da sojojin Myanmar sukayi masu shekaru biyar da suka gabata.
 
A lokacin ‘yan Rohingya kimanin 750,000 ne sukayi kaura daga jihar Rakhine zuwa iyakar Bangaladesh, domin gujewa kisan kiyashin sojojin na Myammar.
 
A ranar 25 ne ga watan Agustan 2017 ne dakarun Myanmar suka kone kauyukan ‘yan Rohingya fiye 300, abinda ya tilastawa ‘yan kabilar wadanda galibi Musulmi kwarara zuwa iyakar Bangladesh.
 
Sansanin na ‘yan Rohingya dake kudu maso gabashin Bangaladesh shi ne wani sansani na ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya.
 

4080710

 

 

captcha