IQNA

A Tsakanin Mutanen Burtaniya:

Muhammad shi ne sunan da yafi shahara a shekarar 2022

16:06 - December 20, 2022
Lambar Labari: 3488365
Tehran (IQNA) A cewar sanarwar Hukumar Kula da Iyali ta Saudiyya, a shekarar 2022 sunan "Muhammad" ya zama sunan da aka fi sani da jarirai maza a duniya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, majalisar kula da harkokin iyali ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa “Muhammad” shi ne sunan da ya fi shahara a duniya.

Wannan majalissar ta jaddada muhimmancin zabar wa jariri suna mai kyau, musamman ma cewa wannan suna zai kasance tare da shi har tsawon rayuwarsa kuma ana daukar wannan sunan a matsayin alama ga mai shi kuma yana taka rawa a cikin halayen mutum.

A cewar wani rahoto da wani kamfanin bincike na Amurka mai suna "Babycenter" ya wallafa, sunan Muhammad ya kasance kan gaba a jerin sunayen da aka fi sani da jarirai maza a Birtaniya a shekarar 2022.

A cikin wannan shekarar, dubun dubatar iyaye sun yi rajistar sunayen ‘ya’yansu a wannan gidan yanar gizon kuma an shirya jerin sunayen mutane 100 da suka shahara a kasar.

Littafin Guinness Book of Records ya sanar shekaru da suka gabata cewa sunan Muhammad ya samu matsayi mafi girma a cikin mutane, yayin da adadin mutanen da ke dauke da wannan suna mai albarka ya kai mutane miliyan 70 a duniya.

A shekarar da ta gabata, wannan kamfanin bincike na Amurka ya sanar da cewa sunan "Muhammad" shi ne sunan da ya fi shahara a tsakanin yara maza da aka haifa a Burtaniya a shekarar 2021.

Kamfanin ya sanar da cewa sunan "Mohammed" yana kan gaba a jerin sunayen jarirai da suka fi shahara a kasar a shekara ta biyar a jere. Sunayen "Nuhu"  da "Oliver"  sun kasance a matsayi na biyu da na uku a cikin jerin sunayen 100 da aka fi sani da jarirai a Birtaniya.

 

4108349

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Burtaniya shahara matsayi na jarirai alama
captcha