Kamfanin dillancin labaran Safa ya habarta cewa, daliban Palasdinawa masu shekaru 10 zuwa 13 sun haddace tare da karanta surar farko na kur’ani a cikin tsarin shirin Baram al-kur’ani a matakin farko. An gudanar da wannan taro ne a makarantar koyon kur’ani ta Annabi Muhammad (SAW) da ke sansanin Nasirat a tsakiyar Gaza.