IQNA

Sanar da shirye-shirye na musamman na Ramadan a Sharjah

19:13 - March 08, 2024
Lambar Labari: 3490767
IQNA - Shugaban sashen kula da harkokin addinin musulunci na Sharjah ya bayyana shirye-shirye na musamman na watan Ramadan, wadanda suka hada da gina sabbin masallatai da kafa tantunan buda baki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sharjah cewa, Abdullah Khalifa Yarouf Al Subosi shugaban sashin kula da harkokin addinin muslunci na birnin Sharjah ya sanar da shirye-shiryen watan Ramadan mai alfarma, wadanda suka hada da ayyuka da al’amura daban-daban na addini da nufin kara wayar da kan al’umma a cikin addini. A cikin waɗannan shirye-shirye na musamman, an yi ƙoƙarin samar da yanayi na ruhaniya da biyan bukatun mutane.

Al-Sabousi ya jaddada cewa, ya zuwa yanzu ma’aikatar ta bude sabbin masallatai 20 a cikin shirinta na gina masallatai 30 a karshen watan Ramadan, wadanda ke da dabaru daban-daban a sassan masarautar. Ƙungiyoyin gyare-gyare, kulawa da tsaftacewa na masallatai suna ci gaba da tantance yanayin waɗannan wuraren. Haka kuma sun yi nazari kan na’urorin sanyaya, hasken wuta da sauti da kuma kara tanti a kusa da masallatai da ke shaida yawan jama’a, sun samar da wuraren da ya kamata ga masu azumi da addu’o’i.

Al-Sabousi ya kara da cewa daya daga cikin shirye-shiryen watan Ramadan mai alfarma shi ne "Sharjah Readers", wanda aka shirya tare da hadin gwiwar "Sharjah Radio Quran". Wannan shiri ya kunshi ma'abota karatu 30 wadanda suke gabatar da sallar tarawihi da tahjudi a masallatai 30 kuma ana watsa su kai tsaye ta kafafen sada zumunta da rediyo na wannan sashe.

Har ila yau wannan sashe yana aiwatar da shirin "Malaman Hadaddiyar Daular Larabawa" tare da hadin gwiwar gidan rediyon Sharjah, inda malamai 30 suka gudanar da wani shiri bayan kammala salla a masallacin Mufalhoun da ke unguwar Mowafijah.

Wannan sashe ya ware masallatai 10 domin gudanar da tafsirin kur’ani da kuma masallatai 20 domin gyaran karatun. Haka kuma za a gudanar da taruka 700 a masallatai da za a mayar da hankali kan haddar kur’ani da koyon hukunce-hukuncen Tajwidi.

Bugu da kari, an fara darussa na ilmantarwa da tambayoyi da amsa ga jama'a da kuma na musamman ga mata a masallatai da dama a birnin Sharjah, wanda manufarsa ita ce wayar da kan al'umma kan hukunce-hukuncen watan Ramadan. Ana kuma gudanar da daruruwan tarurrukan addini da tafsirin Alkur'ani ta yanar gizo.

Sashen ya kuma kebe masallatai na musamman ga al’ummomin da ba sa jin harshen Larabci inda ake gudanar da darussa da tattaunawa a cikin watan Ramadan cikin harsunan Ingilishi da Urdu da Malayalam.

Kafa tantuna da dama na buda baki a yankuna daban-daban na Masarautar Sharjah domin yi wa masu azumi hidima na daya daga cikin ayyukan wannan masarauta.

 

4203997

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: watan ramadan addini kulawa bukatu mai alfarma
captcha